Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu, ya bayyana labarin yadda aka kai masa wani harin da aka yi da niyyar halaka shi, halaka matar sa da kuma dan sa.
Ya bayyana wannan labari ne ta bakin Kakakin Yada Larabai na sa, Uche Ani chukwu, wanda ya fitar da bayani a ranar Talata.
Jim kadan bayan fara taron majalisa a ranar Talata, Ekweremadu ya nemi amincewar sauran sanatoci domin ya tashi ya bada labarin yadda ya tsallake rijiya daga yunkurin halaka shi da wasu makasa suka kusa yi.
Sai dai kuma Ekweremadu ya ce ba zai yi dogon bayani ba, domin kada maganar da zai yi ta kawo tangarda ga binciken da ‘yan sanda ke kan yi.
Duk da haka, mataimakin shugaban na majalisar dattawa ya nuna matukar damuwar sa dangane da yadda ‘yan sanda ke tafiyar da binciken.
“Abin haushi, na kira Sufeto Janar, amma wayar sa a rufe. Na kira makusantan sa, ba su dauka ba. Na kira DIG, shi ma bai dauka ba, kuma har zuwa yanzu da na ke maganar nan, babu ko jami’i daya daga cikin su da ya kira ni.
“Na sa mutane na sun kira DPO na yankin Apo. Ba mu gan shi ba sai wajen 5:30 na asubahi, shi ma ba shi ne ya je ba, 2IC din sa ya aika. Ya je ya ga muggan makaman da aka kama da suka gudu suka bari. Shi ma ya koma, daga baya ya aiko cewa DPO zai zo da kan sa. Ni dai har na baro gida na da karfe 9:30, DPO bai je ba.”
Kokarin da PREMIUM TIMES ta yi domin jin ta bakin ‘yan sanda ya ci tura. Kakakin su bai amsa kira ba, kuma bai maida amsar sakon tes ba.
Amma Kwamishinan ‘Yan Sanda na Abuja, Bala Ciroma, ya shaida cewa shi dai har lokacin da ake masa wannan tambayar, bai samu wani rahoton kai farmakin neman halaka Ekweremadu ba.
Tuni dai aka fara yin tir da wannan hari da aka kai gidan Ekweremadu, cikin wadanda suka nuna damuwa kuwa, har da Kakakin Majlisar Tarayya, Yakubu Dogara.
Discussion about this post