BINCIKE: Jariran da ake haihuwa da mazan da suka kwana biyu kan yi fama da rashin lafiya a tsawon rayuwan su

0

Wasu likitoci a jami’ar Stanford dake gudanar da bincike a California kasar Amurka sun bayyana cewa jariran da ake haihuwa tare da mazan da suka kwqna biyu na samun matsaloli da dama da kan yi wa kiwon lafiyar su lahani.

Likitocin sun gano haka ne a wani binciken da suka gudanar da maniyin maza miliyan 40 masu shekaru 25; 25 zuwa 34; 35 zuwa 44; 45 zuwa 55 da sama da shekaru 55.

Sakamakon binciken da suka samu ya nuna cewa jariran da mahaifan su maza suka fara tsufa kan sami matsalolin kiwon lafiya kamar su suma da rashin nauyi kamar sauran ya’yan.

Binciken ya kara nuna cewa matan da suka haifi wadannan jarirai kan kamu da cutar siga.

Likitocin sun bayyana cewa hakan na yiwuwa ne saboda matsalolin dakan kama namiji a dalilin tsufa sannan shantaba da giya kan kawo irin haka.

Likitocin sun bayyana cewa bisa ga sakamakon binciken yaran da za su yi fama da wannan matsalar basu da yawa amma sun yi kira ga maza da su ringa kula da kiwon lafiyar su musamman kafin su yi aure domin guje wa haka.

Sun ce yin hakan zai taimaka wajen haifo yara cikin koshin kiwon lafiya sannan da kare mata iyayen su daga kamuwa da cutar siga.

Share.

game da Author