Kungiyar malama kwalejojin koyar da aikin malunta reshen jihar Neja (COEASU) sun fara yajin aiki domin nuna fushinsu kan rashin kammala biyan bukatun su da gwamnati ta ki yi.
Shugaban kungiyar Danjuma Beji ya sanar da haka wa manema labarai ranar Laraba a Minna.
Beji ya bayyana cewa har yanzu kashi 77.3 bisa 100 ne daga cikin bukatun su gwamnati ta iya biya sannan shi ko kashi 23.7 shiru har yanzu basu ce komai a kai ba.
” Har yanzu gwamnati bata amince da Karin shekarun yin ritayan malamai ba wato shekaru 65 da amfani da sabon tsarin biyan albashin malamai na CONPCASS.
” Gwamnati ta bar mu cikin tsofaffin kayan aiki da gini sannan gashi muna fama da karancin malamai da ma’aikata a kwalejin.
Beji yace abin takaici shine yadda gwamnati ta yi kunnen uwar shegu da wadannan matsaloli na su duk da wasiku da wa’adin da suka bata.
A karshe sakataren COASU Mohammed Kolo ya yi kira ga gwamnati da ta yi abin da ya kamata musamman yadda kungiyar ta lashi takobin kin komawa aiki har sai gwamnati ta biya bukatun ta.