Dokar kiwon lafiya ta kasa doka ce da a aka shirya domin inganta fannin kiwon lafiya a kasa Najeriya da kuma tsara yadda mutane za su rika samun ingantaccen kula a asibitoci tare da bin doka yadda ya kamata.
Shi dai wannan doka an kafa shi a zamanin mulkin gwamnati da ta shude, a mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a ranar 1 ga watan October 2014.
A daidai wasu daga cikin masu fada aji a fannin kiwon lafiya suna korafin cewa gwamnati na kin bin wannan doka sau da kafa, ita gwamnati ta kafe kan cewa lallai tana aiwatar da hukunce-hukuncen da ke tattare a cikin wannan tsare-tsare da wannan doka ya ayyana.
Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa dokar kiwon lafiya na aiki yadda ya kamata. Sai dai ya ce maganar ware kashi daya bisa 100 na kasafin kudin Najeriya wa fannin kiwon lafiya bai samu tsallakewa ba har yanzu.
Yadda tsarin dokar Kiwon Lafiya ta kasa yake. Shin hakkin tabbatar da ganin an aiwatar da dokar kiwon lafiya a Najeriya ya rataya a kan wa nene?
PREMIUM TIMES ta gana da wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya da masana dokoki domin samun bayanai kan wanda ke da ikon aiwatar da dokar kiwon lafiya.
Sabon shugaban kungiyar likitoci (NMA) Francis Faduyile ya bayyana cewa ikon kafa wannan doka na ma’aikatar kiwon lafiya ne a madadin gwamnati amma sai gashi gwamnati bata ce komia a kai ba.
Faduyile ya ce fannin kiwon lafiya za ta farfado idan kasar nan ta dace da gwamnatin dake da kishin kasar da za ta tabbatar cewa duk sashen dokar na aiki yadda ya kamata.
Shi kuwa Nzube Akunne masanin dokoki amincewa da Faduyile yayi inda ya bayyana cewa rashin bin dokar babban matsalane a kasa. Sannan ya kara da cewa da za samu a iya ganin dokar tana aiki yadda ya kamata da matsalolin fannin kiwon lafiya a kasar nan ya zama tarihi.
Shi ko ma’aikacin kiwon lafiya Henry Ewononu cewa yayi, ci gaba da yi wa mutane hudubar wannan doka da amrfanin ta shima zai taimaka wajen ganin an samu nasara. Da kuma ganin gwamnati ta amince da ware wannan kaso da ake ta neman tayi wa fannin kiwon lafiya a kasafin kudi.