Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rage kudaden siyan fom din jarabawar kammala makarantar Sakandare wato NECO SSCE da na shiga manyan makarantun kasar nan, JAMB UTME da jarabawar BECE.
Mai taimakawa shugaban Kasa a sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad ne ya bayyana haka a shafin sa na Tiwita.
Bashir ya ce daga yanzu za a saida fom din jarabawar JAMB ne kan naira 3,500 ba kamar yadda yake a da ba naira 5000, sannan kuma NECO yanzu ya koma naira 9,850.
Hakan zai fara aiki ne daga watan Janairun 2019.
Discussion about this post