Kotu ta umurci gwamnatin jihar Kano ta dawo da ma’aikata 894 aiki

0

Kotun kare hakkin ma’aikata a jihar Kano ta umurci gwamnatin jihar da ta dawo da ma’aikatan kiwon lafiya 894 da ta kora da wadanda aka canja wa wuraren ayyuka.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne bisa ga karan da wadannan ma’aikata suka shigar a ranar 3 ga watan Yulin 2017.

Lauyan da ya shigar da karan Surajo Ali ya bayyana a kotu cewa shugaban aiyukka a madadin gwamnatin jihar Kano ya canja wa ma’aikatan fannin kiwon lafiya 894 wurin aiki sannan aka canja musu tsarin biyan albashin daga CONHESS zuwa HAPSSS.

Ali ya ce bisa ga doka shugaban aiyukka bashi da ikon yin haka domin wannan iko na hukumar kula da aiyukkan asibitoci.

A karshe alkalin kotun Judge E. Isiele ya yanke hukuncin cewa gwamnatin jihar Kano ta dawo da wadannan ma’aikata aiyukkan su da suke yi a da.

Isiele yace gwamnati za ta biya ma’aikatan sauran albashin su da ta zaftare a dalilin canja musu tsarin biyan su albashi daga CONHESS zuwa HAPSSS na tsawon watanni 27 da ta yi sannan ta ci gaba da biyan su da tsarin biyan albashi na CONHESS.

Share.

game da Author