” Ku rage kashe kudade barkatai” –Gargadin Gwamnatin Tarayya ga jihohi

0

Gwamnatin Tarayya ta gargadi jihohi da su zaftare duk wasu hanyoyin da suke kashe kudaden da ba su da wani tasiri, sannan kuma ku bijiro da hanyoyin samun kudaden shiga daga cikin jhohin.

Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed ce ta yi wannan jawabi a jiya Litinin, lokacin da ta ke jawabi a Kaduna, a wuri Taron Majalisar Tattalin Kudade da Inganta Arzikin Kasa (NACOFED), a Kaduna.

Zainab ta ce matsawar jihohi ba su rage gabzar kudade su na kashewa barkatai ba, kuma ba su kara fito da hanyoyin samun kudaden shiga daga cikin jihohin su kan su ba, to babu yadda za a yi su iya daukar nauyin gudanar da dukkan bukatun da jihohin su ke nema na tilas.

Ta ce saboda faduwar darajar farashin man fetur a shekarun da suka gabata zuwa yanzu, gwamnatin tarayya ba ta iya samar wa jihohi da kananan hukumomi isassun kudade daga ribar man fetur da ake kasaftawa a kowane karshen wata.

Ministar ta ce hakan kuwa na faruwa ne saboda a kasar nan kowa ya dogara da ribar man fetur, alhai kuma ga sauran albarkatun kasa nan birjik, wadanda idan aka sarrafa su za a samu kudaden shiga masu tarin yawa.

Share.

game da Author