Jami’in yada labarai na kwalejin koya da aikin malunta dake Gidan Waya jihar Kaduna Danladi Aduwu ya sanar cewa an rufe karatu a makarantar har sai ‘illa masha Allah’ a dalilin zanga-zanga da daliban makarantar suka yi.
” A dalilin haka muke kira ga duk daliban makarantar nan da su gaggabta barin makarantar tun da wuri.
Wani dalibin makarantar da baya so a fadi sunan sa ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa dalibai sun gudanar da zanga zanga ne saboda canja ranar rubuta jarabawa da makarantar ta yi.
” Daliban mataki uku ne suka yi wannan zanga zanga sannan kuma da rade-radin wai kila za akara kudin makaranta.
Babu wanda ya ji rauni a zanga-zangar sai dai hukumar makarantar sun rufe makarantar zuwa wani lokaci.