Sanatan dake wakiltar Gombe ta Kudu Joshua Lidani ya canja sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Sanata Ahmad Lawan ne ya bayyana haka a zauren majalisar dattawa ranar Laraba.
Sai dai a yayin da yake sanar wa majalisar haka, ya ce Lidani bai fadi dalilan da ya sa ya canja Shekar ba.
Idan ba a manta ba a dan kwanakin nan anyi ta samun ‘yan majalisa suna canja sheka.