Ina kalubalantar El-Rufai, Ashiru da duk dan takarar gwamna a Kaduna su zo mu gwabza a muharawa – Haruna Saeed

0

Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar SDP, Haruna Saeed, ya kalubalanci gwamna Nasiru El-Rufai na Jam’iyyar APC, Isa Ashiru na PDP da duk wani dan takarar gwamna a jihar Kaduna da ya zo su gwabza a muhawara idan da gaske su ke yi.

Haruna Saeed wanda shine dan takarar jam’iyyar CPC a zaben 2011 ya canja sheka ne daga jam’iyyar bayan ta rikide ta zama APC bisa kokawa da yayi na rashin iya shugabanci da ya yi wa jam’iyyar katutu.

Haruna ya ce kyan dan takara ya fito bainar jama’a ya fede biri daga kai har wutsiya, ya fadi wa mutanen da zai mulka irin shirye-shiryen da yake musu da irin abin da ya yi a da.

” Abu na farko da mutane kan so su sani game da dan takara shine menene ya kunso musu da zai sa su mara masa baya.

” Zai iya zama nagartaccen shugaba amma kuma mutane ba za su iya tantance haka ba sai ya tsaya, gashi ga sauran ‘yan takara sun goga kowa ya bayyana manufofin sa sannan ne za a san waye gwani.

Bayan haka Haruna ya kara da cewa babban dalilin da ya sa ya fice daga APC shine ganin yadda magoya bayan sa suke ta yi masa kiraye-kiraye da ya fito ya yi takarar gwamnan jihar.

” Ita PDP dama can an san ta riga ta ragwargwabe, duk da cewa ba wai jam’iyyar bace ta lalace, wadanda suke cikin ta ne kuma har yanzu sune a ciki ba ta canja ba.

” Ita ko APC tun farko shugabanci ne babban matsalarta. Wasu sun yi katutu a cikin ta inda suke hana ruwa gudu. Hakan yasa sai yadda wasu ke so ba yadda ya kamata ba.

Share.

game da Author