Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas Chike Oti ya bayyana cewa rundunar ta kama wani dan kasar Togo mai suna Sunday Adefonou da ya caki dan Najeriya da wuka sau uku a kirji.
Oti ya bayyana cewa an kama Adeonou mai shekaru 22 ranar 2 ga watan Nuwamba bayan ya aikata wannan ta’asa ranar 31 ga watan Oktoba a cikin gidan dan Najeriya mai suna Opeyemi Bademousi.
” Bademosi ya dauki Adefonou a matsayin mai yi masa girkin abinci ne a gidan sa a ranar 28 ga watan Oktoba inda bayan kwanaki uku Adefonou ya nemi ya yi masa satan kudi.
” Adefonou ya caka wa Bademosi wuka sau uku a kirjinsa bayan ya nemi tsabar kudi bai samu ba sannan ya cika wa wandonsa iska zuwa jihar Ondo.
Oti yace sun sami nasarar kama Adefonou a dalilin binciken da suka gudanar bayan sun saurari karan mutuwar Bademosi daga bakin matarsa Ebunola.
A karshe Oti ya jinjina wa kokarin da ma’aiakatan sa suka yi sannan da hadin kan da mutanen jihar Legas suka basu a lokacin da suke gudanar da wannan bincike.