APC ta kori Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Shiyyar Arewa Maso Yamma, Inuwa Abdulkadir

0

Jam’iyyar APC Reshen Jihar Sokoto ta kori Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Shiyyar Arewa Maso Yamma, Inuwa Abdulkadir.

Korar ta sa ta biyo bayan wani rubutaccen korafi da daya daga cikin ‘yan jam’iyyar APC da ke mazaba daya da Inuwa, ta Magajin Gari Ward A, mai suna Na’ibi Abubakar ya rubuta kuma ya aika wa uwar jam’iyyar ta jihar Sokoto.

An zargi Inuwa mai lambar rajista da APC ta SOK/SON/04006510 da aikata laifukan da aka ce duk yi wa jam’iyya zagon-kasa ne, tozarta ta da kuma rashin maida hankali kan kulawa da hidimta wa jam’iyya.

Daga cikin zargin da Na’ibi Abubakar ya yi wa Inuwa, sun hada da:

Bai taba zuwa ya halarci taro ko da sau daya ba kan yadda za a shirya zabukan fidda-gwani na fitar da ‘yan takarar zaben 2019 na APC a kowane mukami na jiha da na kasa.

Bai halarci taron zaben fidda-gwanin APC na dan takarar shugaban kasa ba, inda APC a jihar Sokoto ta zabi Shugaba Muhammadu Buhari.

Inuwa bai halarci zaben fidda-gwani na dan takarar gwamnan jihar Sokoto da APC ta tsaida Mataimakin Gwamnan Sokoto ba.

Inuwa ya tozarta jihar APC reshen jihar Sokoto tare da bada wa Shugaba Muhammadu Buhari kasa a ido, ta hanyar kin halartar zabe na musamman da aka kaddamar da mubayi’ar mika takarar shugaban kasa ga Muhammadu Buhari sunkutukum.

Inuwa ya taba shaida wa taron wasu mutane cewa Mataimakin Gawamnan Sokoto, Ahmad Aliyu, ba shi ne shugaba kuma jagoran APC a jihar Sokoto ba.

Inuwa ya taba shaida wa wasu ‘yan jam’iyya cewa Sanata Aliyu Wamakko bay a cikin jiga-jigan jam’iyyar APC a Sokoto.

Tunda Gwamna Aminu Tambuwal ya koma PDP, Inuwa bai taba fitowa ya nuna rabautar sa da nuna daina kusantar gwamnan ba.

Inuwa ya taba shaida wa gungun jama’a cewa har yanzu babu jigo a siyasar Sokoto sai Gwamna Tambuwal.

Har yanzu Inuwa ya na nuna kusancin sa da Tambuwal da kuma sinsinar PDP da ya ke yi, domin har yau bai ajiye mukamin sa na Shugaban Hukumar Gudanarwar Jami’ar Jihar Sokoto ba, mukamin da Tambuwal ya nada shi, a lokacin da gwamnan ke cikin jam’iyyar APC.

An kafa kwamitin da ya binciki wadannan zarge-zarge da aka yi wa Inuwa, kuma kwamiti duk ya tabbatar da gaskiyar haka.
Wannan ce ta sa gaba dayan Mambobin Kwamitin Gudanarwar APC na jihar Sokoto su arba’in su ka sa hannun amincewa a kore shi.

Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta tuntubi Kakakin Yada Labarai na APC na Kasa baki daya, Lanre Issa-Onilu, ya bayyana cewa duk da dai bai karanta wasikar da kwaminitin gudanarwa na jihar su 40 suka turo wa uwar jam’iyya ta kasa ba tukunna, to ya san dai ba su da karfin ikon korar sa.

Ya ce Inuwa zababben mataimakin shugaba ne da kasa baki daya, don haka batun korar sa daga jam’iyya sai dai daga mataki na kasa baki daya.

INUWA ABDULKADIR

Shi kuwa Inuwa da aka kora ya bayyana cewa karamar hukumar sa ba ta da ikon korar sa daga jam’iyya sannan ya ce ko a dalilan da suka bayar babu daya dake da ke da kamshin gaskiya a ciki.

Inuwa ya ce da gangar wasu suka kirkiro sunayen karya domin su ci masa mutunci. Bayan haka ya bada wasu dalilai masu yawa wanda ya ce sune hujjojin sa na aikata wasu daga cikin abubuwan da aka tuhumesa da su.

Share.

game da Author