An sake yi wa matafiya kwanton bauna a Filato

0

An sake yi wa matafiya kwanton bauna a jihar Filato har aka kashe mutane biyu, aka ji wa wasu da dama, a ranar Lahadi da ta gabata, a kauyen Nding cikin Karamar Hukumar Barikin Ladi, cikin jihar Filato. Haka jami’ai suka bayyana.

Wadanda aka kashe din an ruwaito cewa ‘yan kasuwar kayan miya ne da ke kan hanyar su ta komawa da cin kasuwa.

An ce wadanda suka kashe su din sun gudu da motar su kirar ‘pick-up’ wadda aka yi wa lodin kayan miya mallakar wadanda aka kashe din.

Wani mai saida kayan miya a kasuwar kayan-Gwari, mai suna Fodio Umar, ya shaida cewa wadanda aka kashe din duk ‘yan kasuwar su ne, kuma mazauna Barkin Ladi ne.

DPO na Barkin Ladi, Umar,ya tabbatar da afkuwar kisan kuma y ace tuni an rufe su washegari da safe.

Kakakin Yada Labaran Yan sandan Filato ya tabbatar wa Premium Times kisan matafiya, kuma ya ce ana bincike.

Jami’in Yada Labarai na Rundunar Sojojin ‘Operation Safe Haven’, Adam Umar, ya ce an kashe matafiyan ne a Nding Sesu, kusa da Kasuwan Dankali.

Kuma jami’an su sun samu labari bayan da abokan kasuwancin mamatan suka kai musu rahoton kisan da aka yi wa ‘yan uwan ma su.

“An garzaya a sauran mutane biyar da aka ji wa ciwo zuwa Babban Asibitin Barkin Ladi.”

“Mu na nan mu na kokarinn duk inda makasan su ka shiga sai mun nemo su mun damke su.” Inji Adam Umar.

Share.

game da Author