2019: Buhari ne ya taya ni zaben mace takarar mataimakiya ta – El-Rufai

0

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya taya shi zaben mace fitowa a matsayin ‘yar takarar mataimakiyar gwamna a zaben 2019 mai zuwa.

Gwamnan ya bayyana haka a cikin wani martani da ya yi a karo na farko, tun bayan bayyana sunan Hadiza Balarabe a matsayin wadda za ta tsaya a matsayin mataimakiyar gwamna.

Ya yi wannan bayani ne a lokacin da ‘yan Karamar Hukumar Sanga, asalin yankin da Hadiza ta fito suka kai masa ziyarar godiyar tsaida ‘yar karamar hukumar su takarar a matsayin mataimakiyar gwamna.

Nasir ya ce kafin ya tsaida ta sai da ya shawarci Buhari tukunna.

Hadiza ita ce Babbar Sakatariyar Hukumar Kula da Lafiya a Matakin farko ta Jihar Kaduna.

Yayin da wasu ke jinjina wa gwamnan dangane da zaben mace da ya yi, da dama kuma na ganin cewa bai kamata a jiha kamar Kaduna ba gwamna Musulmi ya dauki mataimakin sa Musulmi a zabe na dimokradiyya.

Amma da ya ke jawabi a gaban tawagar Karamar Hukumar Sanga, El-Rufai ya yi karin haske dangane da yadda ya ki daukar Kiristoci ya dauki Musulma daga cikin mutane 32 da ya ce an gabatar masa da sunayen su.

“Sunayen mutane 32 aka kawo mana, cikin su kuwa har da sunayen wasu da muke zaune tare da su a nan. Daga nan muka tsame sunayen wasu muka bar 17, daga nan kuma muka kara tantance 12, daga 12 muka tsame bakwai, muka bar biyar kacal, wato maza uku, mata biyu.

“Dama mu idan mu na tattauna warware wata maslaha mai muhimmanci, na kan tuntubi Shugaba Muhammadu Buhari.
“To sai ya ce min kada na sake na dauki wanda ya fi ni shekaru. Daga nan sai muka cire sunan mutum guda, saura hudu kenan, biyu maza, biyu mata.

Hadiza Balarabe

Hadiza Balarabe

“Daga nan sai ya ce min tunda dai kai hankalin ka ya fi karkata a kan mace, to ka dauki wacce ta fi cancanta a cikin su. To kun ji yadda aka yin a dauki Hadiza, domin ita ce ta fi cancanta.

Daga nan kuma sai ya maida raddi akan masu sukar sa cewa a karon farko a Arewa maso Yamma shi ne ya fara daukar mace mataimakiyar gwamna a zabe. Kuma Musulma ce a jihar da Kiristoci ke da matukar yawa su ma.

Ya ce shi ba zai taba nada mukami a kan wani saboda kabilanci ko dalili na addini ba. Shi cancanta ya ke bi kawai.

Daga nan sai ya ce duk masu sukar sa ai ba su ne suka zabe shi ba. Kuma idan ana ganin ya kwafsa, to me ya sa masu adawa za su fi damuwa, ai da sai su yi shiru tunda kwafsawar da ya yi din su za ta amfana a siyasance, idan ma kwafsawar ya yi.

Share.

game da Author