Tsohon Babban Mai Shari’a, Kutigi ya rasu

0

Tsohon Babban Mai Shari’a, Idris Legbo Kutigi ya rasu, yau Lahadi.

Ya rasu a wani asibiti da ke Landan, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Babban dan sa Sani Kutigi ne ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai labarin rasuwar mahaifin na su.

An haifi Kutigi a ranar 31 Ga Disamba, 1939, ya rasu ya bar ‘ya’ya 18 da jikoki 40.

Shi ne Babban Mai Shari’a na Kasa tsakanin July, 2007 zuwa Disamba, 2009.
Ana sa ran isowar gawar sa gobe domin yi masa jana’iza.

Share.

game da Author