Boko Haram sun banka wa kauyuka biyu wuta, sun kashe mutane da dama

0

Boko Haram sun kai wa wasu kauyuka biyu mummunan hari inda suka kashe mutane da yawa, kuma suka banka wa kauyukan wuta, gidaje da dama suka kone.

An kai harin ne ranar Asabar da dare a Mairari da Fenari, cikin Karamar Hukumar Konduga da ke Jihar Barno.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa maharan sun isa kauyukan da misalin karfe 8:30 na dare, inda suka banka wa gidaje wuta, kuma suka gudu da kayan abinci.

Wannan hari ya faru ne awa sha biyu bayan da Boko Haram suka kashe wasu manoma 10 kuma suka gudu da wasu a kauyen Kuwa-Yangeya, kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa, ranar Asabar din.

Wanda aka kai harin a kan idon sa mai suna Goni Umar ya tabbatar da cewa Boko Haram sun kai harin ne suna cike da motoci da kuma wasu dauke da manyan bindigogi a kan babura.

Shi ma Kwamandan Riko na Bataliya ta 7, Burgediya Janar Bulama Biu ya tabbatar da kai harin, amma ya ce sojoji sun kore su.

Share.

game da Author