Tun kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki, kusan kowa a kasar nan ya san alkiblar da ya dosa idan har ya samu sanarar zama shugaban kasa. Bayan ya yi nasara kuma ya kara jaddadawa cewa batun cin hana cin hanci da rashawa na a sahun gaba wajen sake gina ingantacciyar Najeriya.
Kafin na fara magana a kan gwamnati, bari na fara a kan shi kan sa Shugaba Buhari. Tun daga watan Disamba,1983 da ya zama shugaba na mulkin soja, har zuwa yau, babu abin da ya fi tsana da kuma kyama kamar barayin kudaden gwamnati, wadanda ake ganin su ne ke kashe tattalin arzikin kasa.
Wannan dalili ne ma aka fi yi masa kallon wanda ya fi kowa cancanta da kawar da tsarin wawurar kudade da cin hanci da rashawa a kasar nan, tare da shimfida adalci, adalci, adalci kamar yadda shi Buhari din ke yawan jaddadawa.
Sai dai kuma daga hawan sa mulki a karo na biyu, a ranar 29 Ga Mayu zuwa yau, matakai da salon da gwamnatin Buhari ke bi wajen yaki da cin hanci da rashawa su na da mutukar daure kai sosai, amma ga wanda ya tsaya ya kalli abin da idon basira sosai.
Bari na tafi kai tsaye cikin wasu dalilan da ya sa na ce ina da shakku a kan yadda ake yaki da cin hanci da rashawa, wanda ni a nawa tunanin za a yi ba sani ba sabo ne.
HARKALLAR BABACHIR LAWAL
An kama Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, dan APC da laifin da ya kamata a ce tuni an gurfanar da shi a kotu an hukunta shi. Tun bayan da aka tsige shi daga gwamnati ya kamata a ce an kama shi, an bincike shi. Amma, ba a yi haka ba. Har yanzu shiru mu ke ji dangane da binciken da Shugaba Buhari ya bada umarnin a yi, kuma a ba shi rahoto a cikin gwaggawa.
BADAKALAR DAWO DA ABDUR-RASHID MAINA
Wannan ba karamin abin kunya ya jawo wa Gwamnatin Buhari ba, kuma ya nuna yadda hukumomin tsaron kasar nan ke damalmala harkokin tsaro da kuma su kan su jami’an gwamnatin Buhari ke tafka bahallatsar kauce ka’ida. Ba a taba tunanin harkallar dawo da Maida za ta faru a gwamnatin Buhari ba. Kusan shekara daya kenan da kafa kwamitin bincike, amma har yau Buhari bai ce ga masu laifi ba, ballantana a hukunta su kuma a kore su.
RUNGUMAR ‘YAN HARKALLA HANNU BI-BIYU
Farkon hawa mulkin Buhari, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio na daya daga cikin wadanda aka kai wa farmaki saboda zargin yadda suka wawure dukiya a lokacin mulkin PDP.
Cikin watan Satumba, 2015, an tura jami’an SSS a gidan sa da ke cikin Gidan Gwamnati a Uyo, inda ya ke zaune bayan ya kammala wa’adin sa.
Kusan dukkan jaridun kasar nan sun buga labarin yadda aka samu tulin miliyoyin daloli da muggan makamai a cikin wani daki. Abin da ya biyo baya daga nan, shi ne zargin sa ko tuhumar sa da ake yi da laifin salwantar da naira bilyan 107. A yayin da ba a san halin da shari’a ko tuhumar da ake wa Akpabio ke ciki ba, tuni ya koma APC, Buhari ya yi masa kyakkaywar karba, kuma ya na cikin sahun gaba na kafa gwamnatin adalci, gwamnatin APC a jihar Akwa Ibom.
Abu mai tayar da hankali a nan shi ne yadda magoya bayan Buhari ke nuna irin muhimmancin Akpabio a gwamnatin Baba mai adalci.
ROTIMI AMAECHI DA ZARGIN KWASHE KUDIN JIHAR RIVERS
Daidai lokacin da zaben 2015 ya gabato, kuma a lokacin tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi ya fice daga PDP ya koma APC, an nada shi Babban Daraktan Kamfen na Buhari/Osinbajo 2015.
Amaechi ya rika saida kamfanoni da manyan kadarorin jihar Rivers ga wani attajiri mai suna Patrick Dele Cole.
Cikin manyan kadarorin da aka sayar masa kuwa har da babbar tashar makamashin gas ta jihar.
Bayan Gwamna Nyesom Wike ya hau mulki, an nada kwamitin bincke, kuma aka gano cewa kusan ilahirin kudaden duk sun salwanta a hannun Amaechi, babu su a cikin asusun gwamnatin Jihar Rivers.
Gwamnatin Jihar ta yi zargin cewa Amaechi ya karkatar da dimbin kudaden a zaben 2019 na Shugaban Kasa.
An kai karar Amaechi a Babbar Kotun Jiha, amma ya garzaya Babbar Kotun Tarayya ya roki kotu ta hana a tuhume shi. Kotu ta ki amincewa da rokon sa, daga nan kuma ya sheka Babbar Kotun Daukaka Kara. A can ma kotu ta ce tilas sai an saurari karar sa da aka shigar.
Amaechi bai hakura ba, sai ya garzaya Kotun Koli. A Kotun Koli an nemi Amaechi ya je ya rubuta bayani. Amma sama da shekara daya kenan, har zuwa farkon watan Satumba da jaridar PREMIUM TIMES ta yi cikakken labari kan zargin da Gwamnatin Rivers ke wa tsohon gwamnan ta Ameachi, har yau bai je Kotun Koli ya yi bayani ba.
A halin yanzu, damuwar gwamnatin Rivers shi ne yadda Amaechi ya daure wa attajirin da ya sayar wa kadarorin gindi ya zama dan takarar gwamnan jihar Rivers, a karkashin jam’iyyar APC.
Hakan inji gwamnatin jihar, ana so ne a rufe duk wata barna da ake zargin Ameachi ya tafka a lokacin da ya ke gwamna.
Tambaya, tsoron me Amaechi ke yi na gurfana a kotu? Ba Hausawa sun ce ciki da gaskiya wuka bata huda shi ba.
TSAKANIN HISABIN FAYEMI DA NA FAYOSE
A lokacin da Ayo Fayose ya zama gwamna a karo na biyu, cikin 2014, ya nada kwamitin binciken gwamnatin da ya kayar, ta Kayode Fayemi, wanda ya sake hawa a yanzu.
Kwamiti ya gano irin kudaden da suka salwanta a lokacin mulkin Fayemi, amma sai ya garzaya kotu. Har yau din nan maganar shikenan kamar an shuka dusa.
Daga karshe an yi wa Fayemi wankan tsarki, ya shiga jam’iyyar APC, aka sake tsaida shi takarar gwamna ya kayar da Fayose.
Tun cikin makon da aka kayar da Fayose Hukumar EFCC ta fara yi masa bi-ta-da-kullin cewa ta na jira da ya sauka ta kama shi a kan zargin salwantar wasu kudade.
Kwana daya bayan Fayose, dan jam’iyyar PDP ya sauka, ya kai kan sa ofishin EFCC. Amma abin mamaki har yau Amaechi dan APC bai je Kotun Koli ya yi bayani ba, kuma an zura masa ido, kuma kudaden da ake nema a hannun sa sun nunka wadanda ake nema a hannun Fayose nunkin-ba-nunkin.
HIKAYAR KEMI ADEOSUN DA TA ADELEKE
PREMIUM TIMES ta fallasa yadda tsohuwar ministar harkokin kudade, Kemi Adeosun ta yi harkallar katin shaidar sahale mata zuwa aikin bautar kasa, NYSC. Da farko gwamnatin Buhari ta kauda kai daga batun, har sai da ta ga kafafen yada labarai da kungiyoyi sun taso gwamnatin a gaba, sannan aka sa ta yi murabus.
A cikin wasikar ban-kwana da ta rubuta, ta yarda da cewa ta aikata laifin, amma ba a bisa sanin ta ba. Kwana daya da sukar ta tac fice daga Najeriya ta koma Ingila, tunda dama haifaffiyar can ce.
Gwamnatin Buhari ba ta kama Kemi ba, ba ta hana ta fita ba, duk kuwa da laifin da ta aikata. Domin idan har ba ta aikata laifin ba, ai babu wani tsananin matsin-lambar da zai sa Buhari ya amince da murabus din na ta.
ADELEKE
Ana zargin dan takarar gwamnan Osun, dan jam’iyyar PDP da mallakar shaidar kammala sakandare ta jabu. Adeleke wanda APC aka kayar a zaben da aka yi cikin watan Satumba da kyar da gumin goshi, bayan ta hada kai da Sanata Omisore, a zaman yanzu hukumar ‘yan sanda za ta gurfanar da shi kotu, ko kuma na ce ta gurfanar da shi.
An tambayi Kakakin Rundunar ’Yan sanda na Kasa, Jimoh Mosheed dalilin da ya sa suka ki gurfanar da Kemi, ‘yar jam’iyyar APC, kuma aka bar ta ta tsere, amma kuma za su gurfanar da Adeleke dan jam’iyyar APC, sai ya ce wai ai babu wanda ya kai musu karar Kemi.
Tambaya ta ga hukumar ‘yan sanda ita ce, shin dama duk laifin da ka aikata halastacce ne kenan idan ba a kai karar ka ba? Duk barnar da suka ga ana tafkawa ba za su kai dauki ba, sai an kai musu rahoto?
TSAKANIN EFCC DA OSHIOMHOLE
Jim kadan bayan saukar tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshimhole, wanda shi ne shugaban APC na yanzu, wani fasto ya rubuta wa EFCC cikakken rahoton korafi da zargin salwantar bilyoyin kudade a hannun Oshiomhole.
Ganin cewa EFCC ba ta yi wani abu ba, mai korafin nan ya ci gaba da matsa lamba sai an binciki Oshimhole. Da ya ga ba zai yi nasara ta wannan bangaren ba, sai ya garzaya kotu, inda cikin makonni biyu da suka gabata kotu ta umarci EFCC da ta kamo Oshimhole a cikin kwana biyar, ta bincike shi, kuma ta gurfanar da shi a kotu.
Nan da nan sai Oshimhole dan APC ya garzaya wata kotu, inda ita kuma kotun ta hana EFCC bincikar sa.
Shin a ina makusantan Buhari da ake zargi da cin bilyoyin kudade suka gaji sheka wa kotu su na hana a bincike su? Anya batun yaki da cin hanci da rashawa bai karkace hanya ba kuwa?
OMISORE DA OBANIKORO
Shekaranjiya Juma’a ne hukumar EFCC ta damka wa Sanata Musili’u Obanikoro, wanda kuma tsohon dan PDP ne fasfo din sa dominn ya fice zuwa kasar Amurka, inda a can kuma shi dan kasa ne, kamar Najeriya.
Laifukan Obanikoro:
Sanata Obanikoro ya koma jam’iyyar APC dauke da tulin laifin karbar naira bilyan 4.7 daga hannun Sambo Dasuki. A cikin kudin ya bai wa Fayose naira bilyan 1.3. Obanikoro ya yarda ya karba, domin har ya maida wa Gawamnatin Tarayya naira milyan 100 kacal. Amma kuma an ba shi fasfo din sa zai fice daga Najeriya zuwa Amurka, da nufin neman magani kwanaki hudu kacal bayan kama Fayose.
Can a gefe daya kuma kotu ba sau daya ba ta ce a kyale Dasuki shi ma ya tafi neman magani, amma gwamnati ta hana, an ki sakin sa.
Laifin Omisore: Omisore
Ana zargin Omisore da karbar naira bilyan 1.3 a hannun Sambo Dasuki, wadanda aka yi zargin cewa da su ya yi takarar gwamna a 2014.
Idan ba a manta ba, a zaben nan na takarar gwamnan Osun, Omisore ne ya zo na uku a karkashin jam’iyyar SDP. Kafin a yi zaben raba-gardama, kusan dukkan jiga-jigan APC da gwamnnonin ta da dama sun je Osun wurin Omisore, suka roke shi ya taimaka wa APC ta ci zabe. A karshe ya ce wa magoya bayan sa su zabi APC ba PDP ba.
To, shi ma wata daya kacal bayan da ya taimaka aka kayar da PDP, hukumar EFCC ta maida masa da fasfo din sa na dama da ‘yancin ficewa zuwa kasashen waje.
Matafiya, a dawo laaaafiya!
MA’ANAR BARAWO A IDON DAN APC
A yau duk irin zargi ko dumu-dumun da aka kama ka da harkalla, idan ka koma APC, to ba ka da laifi. Tun kafin a yanke wa tsohon gwamnan Kano hukunci ake ce masa ‘‘Malam ya ci kudin makamai.” A yanzu da ya koma APC kuma, kotu ba ta kai ga yanke masa hukunci ba, amma tuni magoya bayan Buhari sun wanke shi.
Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar kallon barawo ake yi masa a lokacin da ya ke PDP. Da ya ja zugar gwamnoni suka koma koma PDP, har ya taimaka wa Buhari da dukiya da lokaci da jirgin sa ya rika kamfen, to a lokacin Atiku ba barawo ba ne.
Amma yanzu da Atiku ya koma PDP ya zama dan takarar sa, har zai kara da Buhari, kakakin kamfen din Buhari ne ma a sahun gaba wajen kiran Atiku barawo?
Babu irin cin mutuncin da ba a yi wa Omisore ba saboda ana zargin ya ci kudi a karkashin PDP. Amma yanzu da ya taimaka wa APC ta ci zaben jihar Osun, ya ma fi sauran talakawan da ke tayar da jijiyar wuyan kishin APC muhimmanci a jam’iyyar.
Duk wata gararumar da ka rarumo ka shiga APC, to za ka tsaya takara. Amma idan ka shiga wata jam’iyya, to sunan ka barawo.
A yanzu dai na fahimci babu mai laifi kewaye da Buhari, sai ranar da suka fice daga APC sannan za a canja musu suna.
Shin wannan wace irin gwamnati ce? Wadannan wadanne irin mabiya ko magoya baya ne?