Majalisar Malaman Tijjaniyya sun ziyarci Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Majalisar Shura ta Mabiya Darikar Tijjaniyya, inda ya sha alwashin tabbatar da kara tsare kasar nan daga mahara da ta’adda a kasar nan.

Ya karbe su a Fadar Shugaban Kasa a jiya Juma’a.

Buhari ya roki shugabannin addini da su ci gaba da yi wa kasa da kuma gwamnati addu’a.

Jagoran ‘yan Tijjaniyya din Ibrahim Maihula ya ce za su ci gaba da yi wa mulkin Buhari addu’a.

Wannan Majalisa ta kai wa Buhari ziyara kwana daya bayan wasu gungun ‘yan wasan kwaikwayo daga Kano da Kaduna sun kai masa ziyarar mubaya’a.

Share.

game da Author