Ma’aikatan Nigeria Airways 900 suka mutu kafin su karbi kudaden fansho

0

Daya daga cikin mambobin kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin tantance ma’aikatan kamfanin Jiragen Sama na Nigeria Airways da suka yi ritaya, ya bayyana cewa, ma’aikatan kamfanin 900 suka mutu ba su kai ga karbar kudaden fansho da na sallamar su aiki ba.

Sha’aibu Alfa, wanda shi ne ke kula da aikin tantancewar a Kano, ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN a Kano.

Ana gudanar da aikin tantance tsoffin ma’aikatan ne a wurare uku.

Ya ce wadannan 900 da suka mutu, duk sun rasa rayukan su ne a cikin shekaru 15, a lokacin da rayuwa ta yi musu kunci, suka kasa biya wa kan su kudaden magani a duk lokutan da rashin lafiya ta same su, gidajen su suka lalace, suka gararin rayuwa.

Alfa wanda shi ne Sakataren Kungiyar Direbobin Jiragen Nigeria Airways, ya jinjina wa Shugaba Muhammadu Buhari bisa ga amincewar da ya yi a biya tsoffin ma’aikatan kamfanin jiragen kudaden su.

Share.

game da Author