Kwararren lauya, Femi Falana, ya bayyana cewa dokar nan ta hana wasu mutane fita kasashen waje da Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa, ba ta a cikin tsarin mulkin Najeriya, don haka haramtacciya ce.
A cikin wata makala da ya rubuta kuma PREMIUM TIMES ta buga a safiyar yau Litinin, Falana ya ce ba sau daya ko sau biyu ba ya sha jan hankalin Buhari cewa idan zai yi yaki da cin hanci da rashawa, to ya tabbatar da cewa ya na yin abin a bisa yadda doka ta tanadar.
Ya ce dokar mai suna “Executive Order 6’’, doka ce wadda kawai za a ce an dawo da irin mulkin karfa-karfa wanda Buhari ya rika yi a zamanin ya na soja.
Falana ya ce idan za a tuna, cikin 1999 Kotun Koli ta yi tir da dokar da jami’an SSS suka kakaba wa lauya Olisa Agbakoba, inda suka kwace masa fasfo suka hana shi fita waje, cewa haramtacciya ce, domin ba su da hurumin da za su tauye wa mutum ‘yancin sa na walwala.
Kotun Koli ta ce haram ne a tauye wa dan Najeriya ‘yancin sa da ke kunshe a cikin kundin tsarin mulki, Sashe na 41, kuma dukkan kasashen Afrika sun yi amanna da wannan daftari, na ‘yancin dan adam da kuma ‘yancin sa na yin walwala.
Falana ya ce babu wata dokar musamman da shugaban kasa zai iya yi domin ya karya wannan kundin tsarin mulki.
Falana ya tunatar da yadda a lokacin mulkin Jonathan aka hana wasu mutane da suka hada Emeka Ojukwu, Nasir El-Rufai, Oby Ezekwesili da Sanunsi Lamido Sanusi fita kasashen waje ta hanyar kwace musu fasfo.
Ya ce El-Rufai da Sanusi Lamido Sanusi, wanda a yanzu shi ne Sarkin Kano, duk sun garzaya kotu, suka kalubalanci dokar, kuma suka yi nasara.
Fitaccen lauyan ya kara da cewa wannan doka da gwamnatin Buhari ta kafa, ta kara nuna cewa gwamnatin ba ta ma san abin da ta ke yi ba.
“Tunda dama can mutane 50 din da aka ce an hana fita, duk shari’ar su ta na kotu, kuma kotu ta karbi fasfo din su ne a matsayin cike wasu sharuddan beli. To babu bukatar kafa wata doka a yanzu kuma a kan su. Domin a duk lokacin da suke da bukatar fita waje a bisa tilas, kamar duba lafiya da makamantan haka, ai su na zuwa kotu su nemi a ba su, izni idan sun dawo kuma su damka shi a kotu.”
A kan haka Falana ya ce kafa wannan doka shirme ce, rashin yin kyakkyawan nazari ne, kuma tozarta gwamnati ce da nuna cewa ba ta ma san abin da ta ke yi ba.
Falana ya ce matsalar gwamnatin Buhari shi ne rashin yin kwakkwaran nazari kafin ta aiwatar da wani hukunci.
Daga nan sai ya tunatar da wannan gwamnatin cewa, a lokacin mulkin Marigayi Umaru ‘Yar’adua, Shugaban SSS ya rubuta wa ofisoshin jakadun kasashen waje cewa kada su sabunta bizar Nuhu Ribadu da Nasir El-Rufai, wadanda a lokacin su na waje su na gudun hijira.
Amma yayin da aka yi gaggawar nuna wa ‘Yar-Adua cewa cikin 1999 SSS sun yi wa Olisa Agbakoba haka, amma Kotun Koli ta yi fatali da dokar da aka kakaba wa Olisa din, nan da nan sai ‘Yar’Adua ya taka wa SSS burki, aka janye batun.
A kan wadannan dalilai da wasu misalai da dama da babban lauyan ya bayar ne ya ce ya kamata Buhari ya gaggauta gaggauta nade tabarmar kunya, soke wannan doka da gaggawa, domin haramtacciya ce.