2019: Zan goyi bayan Atiku don ya kayar da Buhari -Wike

0

Gwamnan Jihar River, Nyesom Wike, ya ce zai bada muhimmin goyon baya domin dan takara shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Wike wanda zaben fidda gwani ya goyi bayan Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, ya bayyana haka ne a Fatakwal, ya na mai cewa ba ya da-na-sanin goyon bayan Tambuwal da ya yi.

“Tabbas Gwamna Tambuwal na goyi baya, kuma ban yi da na sani ba. Amma jam’iyya ta zabi wanda ta fi so, don haka ni mai biyayya ne ga jam’iyya. Zan goya wa Atiku Abubakar baya domin ya yi nasara a zaben 2019.”

Haka wata sanarwa ta bayyana daga Gidan Gwamnatin Jihar, a Fatakwal.

Sanarwar ta ce Wike ya fadi haka ne a wurin wani taron nuna godiya da shukura dangane da kammala taron gangamin zaben dan takarar shugaban kasa a jihar Rivers din ta karbi bakuncin kammalawa lafiya a makon da ya gabata, wanda Atiku ya yi nasara.

Kakakin yada labaran Gwamna Wike, mai suna Simeon Nwakaudu ne ya saw a takardar hannu.

Share.

game da Author