Janar na soja ya bada shawarar yadda za a magance rikicin Filato

0

Kwamandan ‘Operation Safe Haven’, Manjo Janar Augustine Agundu, ya kawo shawarar hanyoyi biyu kadai da ya ce za a iya bi a kawo karshen kashe-kashen da ake faman yi tsawon shekaru 18 a jihar Filato.

Agundu ya ce idan ba a yi amfani da wadannan shawarwari ba, to kuwa rikicin ba zai taba kawo karshe ba.

Ya ce idan ba a yi amfani da wadannan shawarwari ba, to duk wani taron tattauna yiwuwar zaman lafiya, zai kasance aikin banza ne kawai.

Daya daga cikin shawarawarin da Manjo Janar din ya bayar shi ne: “duk wani gungun masu kashe-kashe su yi saranda da dukkan makaman da ke hannun su, saboda a fili ta ke cewa kowa ma ya sani, duk wadannan matasa sun mallaki makamai kuma muggan makamai sosai.”

Ya ce sun fahimci haka daga irin zaman sasantawa da sojojin suka rika yi a baya.

Abu na biyu kuma shi ne ‘yan siyasa da sarakunan gargajiya da shugabannin addinai tilas su rika shiga lunguna da sako-sako su na kai nasihar cewa kowa ya rungumi zaman lafiya, a daina rikici.

Agundu ya bada wadannan shawarwari ne a lokacin da ake gudanar da wani taron gaggawa da Cibiyar Kokarin Wanzar da Zaman Lafiya ta DREP ta shirya a Karamar Hukumar Jos ta Kudu.

An shirya taron ne domin neman samun mafitar kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihar wanda ya samo asali tun cikin 2001, kuma ya yi sanadiyyar asarar daruruwan jama’a, ciki har da jami’an tsaro da dama.

“Tilas idan ana so a zauna lafiya, to dukkan matasan kowace kabila da ke da muggan makamai a hannun su, sai sun yi saranda din makaman ga hukuma tukunna.”

Shi kuma Gwamna Simon Lalong, wanda ya halarci taron, ya dora laifin rikice-rikicen a kan ‘yan siyasa.

“Idan mun ce siyasa ce ke haddasa rikicin wasu ba yarda suke yi ba. Amma duk siyasa ce. A cikin masu sarautun gargajiya da shugabannin addinai akwai ‘yan siyasa a cikin su. To idan batun siyasa ya taso, shi dan siyasa zai iya yin komai domin ya cimma biyan bukatar sa.’’ Inji Gwamna Lalong.

Share.

game da Author