Shugaban jam’iyyar APC Adam Oshiomhole ya bayyana cewa tabbas jam’iyyar za ta mika duka ‘yan takarar jam’iyyar kafin ranar 18 ga watan Oktoba kamar yadda take a dokar hukumar.
” Ba mu karya doka ba har yanzu. Doka ta ba mu har zuwa ranar 18 mu mika ‘yan takaran mu kuma haka za mu yi.
Idan ba a manta ba hukumar Zabe, INEC ta haramta wa Jam’iyyar APC fitar da sunayen ‘yan takarar dukkan mukamai a zaben 2019, kamar yadda PREMIUM TIMES ta tabbatar da wannan rahoto na musamman a yau.
Hakan ya faru ne saboda jam’iyyar ta kasa cika ka’idojin wa’adin gudanar da zaben fidda-gwanin ‘yan takara ya zuwa ranar 7 Ga Oktoba, kamar yadda dokar zabe ta tanadar.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa tuni ta sanar da Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshimhole wannan sanarwa, a cikin wata wasika da ta aika masa a ranar Talata, wacce PREMIUM TIMES ta ga wasikar da idon ta jiya Talata da yamma.
Jam’iyyar APC a jihar Zamfara dai ta shiga rikici ne bayan darewar da ta yi gida biyu, har abin ya kai su ga mummunan tashin hankalin da har tawagar gwamna Abdul’aziz Yari ya sha jifa daga hannun wasu hasalallun matasan jam’iyyar.
Rikicin dai ya taso ne daga bangaren gwamna da kuma na Sanata Kabiru Mafara.
Shi da Yari ya yi ta kokarin ko ta halin kaka ya ga cewa wanda ya ke so, Mukhtar Idris shi ne ya gaje shi a mulkin jihar Zamfara.
Wannan ne ya sa ya samu tirjiya daga bangaren Sanata Marafa, wadanda suka ki yarda da dauki dorar da Yari ya yi na dora Idris a matsayin dan takara ba tare da an yi zaben fidda gwani ba.
APC ta kasa ta rushe shugabannin jam’iyyar na jihar Zamfara, kuma ta umarci Yari, wanda shi ma dan takarar sanata ne, ya tsame hannun sa daga harkokin jam’iyyar kwata-kwata.
Wannan ne ya haifar da wata sabuwar rashin jituwa tsakanin Oshimhole da Mataimakin sa, Lawal Shu’aibu.
Bangaren Yari ya shirya zaben ‘yan takara da kan sa, inda uwar jam’iyya ta kasa ta ce ba ta amince da zaben ba.
Kwamitin shirya zaben da uwar jam’iyya ta kasa ta tura a jihar ya dawo da rahoton cewa bai samu damar shirya zabe a jihar ba.
A yanzu da INEC ta shaida wa Shugaban Jam’iyya, Adams Oshiomhole cewa kada ma ya bata lokacin aiko da sunayen ‘yan takarar kowane mukami daga jihar Zamfara, saboda ba a gudanar da zabe a cikin kayyadajjen lokacin da hukumar a gindaya ba.
INEC ta tunatar da Oshimhole cewa tun cikin watan Janairu, 2018 ta fitar da jadawalin hada-hadar zabe, wanda ta ce za a gudanar da zabukan fidda-gwani daga ranar 18 Ga Agusta zuwa 7 Ga Oktoba.
“Duk da wannan sanarwa da INEC ta fitar tun a farkon shekara, amma rahoton da ofishin INEC daga jihar Zamfara ya aiko mana ya nuna cewa ba a yi zaben fidda-gwani a jihar Zamfara ba. Duk kuwa da cewa mun tura wakilan mu shirye da nufin su je a yi zaben.
INEC ta ce a bisa hujjojin da ke shimfide a cikin Dokar Zabe ta 87 da ta 31 ta 2010, wanda aka yi wa kwaskwarima, “INEC ba ta jiran jam’iyyar ka ta kawo mata sunayen ‘yan takarar kowane mukamin siyasa daga jihar Zamfara.
“Bari mu kara yin dalla-dalla, jam’iyyar APC ba za ta shiga takarar zaben gwamna, zaben majalisar dattawa, na majalisar tarayya da na majalisar dokoki ba a jihar Zamfara, a 2019.”
Sakataren Riko na INEC, Okechukwu Ndeche ne ya sa wa wasikar hannu.
Wannan mataki da INEC ta dauka, ya bai wa jam’iyyar PDP babbar damar lashe zaben jihar zamfara a dukkan matakai.
Kuma wannan ne karo na farko da PDP za ta yi nasara a jihar, tun bayan dawowar mulkin dimokradiyya, cikin 1999.
Tuni dai PDP ta tsaida Bello Matawalle a matsayin dan takarar gwamnan jihar.