Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi kira ga gwamnatocin duniya kan a kara ware kudade domin samar wa mutanen kasashen su dakunan bahaya.
WHO ta bayyana cewa rashin tsaftace muhalli, rashin bandakuna da rashin tsaftataccen ruwa na daga cikin matsalolin dake cutar da kiwon lafiyar mutane a kasashe da dama.
Shirin muradin karni na shida shine samar da tsaftataccen ruwa da muhalli ga kowa kafin 2030.
” Bincike ya nuna cewa a dalilin rashin daukan mataki kan hana yin bahaya a waje da rashin samar da tsaftataccen ruwan sha, Najeriya na daga cikin kasashen duniya da wannan matsalar ya zama mata ruwan dare.
WHO ta ce a dalilin haka zata hada hannu da Najeriya domin tsaro hanyoyin kawar da mutuwar mutane 829,000 da ake samu duk shekara a kasar a dalilin cututtukan da yin bahaya a waje da rashin tsaftatacen ruwa ke kawo wa.