Ganduje ya musanta karbar toshiyar-bakin dala milyan biyar a hannun ‘yan kwangila

0

Gwamnan Kano Umar Ganduje ya yi barazanar maka wata jaridar online kara kotu, bayan da jaridar ta buga labarin cewa ya karbi toshiyar-bakin dala miliyan 5 a hannun ‘yan kwangila.

Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Mohammed Garba ya fitar kuma ya sa wa hannu a madadin gwamnatin jihar, ya ce ‘yan adawa ne suka hautsina bidiyon da aka ce wai shi ne ke karbar kudi, domin kawai su bata wa Ganduje suna.

Garba ya ce an fitar da bidiyon a daidai lokacin da wasu fittattun ‘yan Najeriya ke ta fadawa tarkon masu hautsina bidiyo su na kirkirar karya da sharri domin su zubar musu da mutunci a bainar jama’a.

An ce dama a baya an yi kokari a shirya wa Ganduje gadar-zare, amma ba a yi nasara ba. Wannan ne ya ce dalilin da ya sa wasu ‘yan adawa suka rura wutar fidda bidiyon a bainar jama’a.

Jaridar Daily Nigerian ce ta buga labarin da farko inda ba ta ambaci sunan gwamnan ba, sai daga baya ta sake bada labarin, tare da buga hoton Ganduje, ta ce shi ne ya karbi toshiyar-bakin daga hannun ‘yan kwangila.

Daily Nigerian ta ce ta na rike da bidiyo uku, wadanda suka nuna yadda Ganduje ya karbi kudaden sau uku. Ya ce bidiyon farko ya nuna Ganduje ya na cusa kusan dala miliyan 3 cikin malum-malum.

Jaridar ta kara da cewa ta bi hanyoyin cikin gida da kuma ta hannun masana daukar finafinai sun tabbatar mata da cewa bidiyon na gaskiya ne, ba kirkirar ko hautsina shi aka yi ba.

Ta kara ce wa harkallar ta fusata Buhari, har ya bada umarnin a gudanar da bincike bayan da kalli bidiyon shi ma.

Jami’an SSS ba su amsa kiran da PREMIUM TIMES ta yi musu domin jin ta bakin su ba.

Sai dai kuma Gwamnatin Kano ta karyata bidiyon ta na mai cewa sharri ne da bi-ta-da-kulli.

“Inda za ku gane sharri ne da yarfe, har yau jaridar ba ta ambaci sunan wanda ya bayar da kudin ba.” Inji Kwamishina Garba.

Wata kafar kare hakkin ‘yan jarida da ke Amurka ta ce za ta shiga gaba wajen kare hakkin Ja’afar Ja’afar, mawallafin jaridar, wanda ta ce a zaman yanzu ya boye, saboda ana yi wa ran sa da lafiyar sa barazana. Don haka ta na jan hankalin jami’an tsaro a kan haka.

Share.

game da Author