‘Yan siyasan Barno na hayan tsageran matasa wajen Kamfen – Rundunar Tsaro na NSCDC

0

Hukumar Tsaro ta NSCDC a jihar Barno ta yi shelar cewa wasu ‘yan siyasa a jihar na yin hayan matasa ‘yan taratsi dauke da muggan makamai domin shirin yakin neman zaben 2019 a jihar.

Kwamandar Rundunar NSCDC na Jihar Barno, Ibrahim Abdullahi ne ya furta haka a Maiduguri, babban birnin jihar ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a yau Talata.

Abdullahi ya ce jami’an sa sun fahimci ambaliya da tudadowar wadannan batagari da tsageran matasa a wuraren kamfen din ‘yan siyasa.

“Ayyukan da irin wadandan ‘yan siyasa ke yi za su iya hargiza zaman lafiyar da aka samu a Maiduguri. Ya kuma yi gargadin cewa ‘yan Boko Haram za su iya sajewa da irin wadannan batagarin matasa domin su rika kai munanan hari.”

Daga nan sai ya ce ya kamata wadannan ‘yan siyasa su fa sani cewa akwai dokar kasar nan shashe na 227 ta kundin tsarin mulki na 1999, da kuma dokokin zabe wadanda za su iya hawa kan su idan su na irin wannan munanan ayyuka.

Share.

game da Author