An sace malaman makarantar Shehu Idris dake Makarfi a hanyar Zariya

0

Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da wasu malaman makarantar koyan aikin Ungozoma da wasu kwasa-kwasai na kiwon lafiya a hanyar su ta zuwa Makarfi daga Zariya.

Kamar yadda wani ma’aikacin makarantar Ahmed Rahama ya shaida wa PREMIUM TIMES, wannan abin takaici ya auku ne ranar Lahadi da yamma a daidai ma’aikatan suna hanyar su na dawowa garin Makarfi daga Zariya.

” Wannan abin Takaici ya dimauta mu matuka a wannan makaranta. Domin kuwa yanzu ana zaman juyayi ne. Bayan masu garkuwan sun kama wadannan malamai sai suka taho marabar Makarfi suka ajiye motar suka tafi da su a wata motar.

Ahmed ya bayyana cewa tuni jami’an ‘yan sanda sun dauke motar zuwa ofishin su dake Makarfi.

Wadanda aka Sace sun hada da darektan kwalejin koyar aikin kula da hakura, Dr Akawu, da Halima, Rabi Dogo.

Share.

game da Author