Zababben Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya bayyana cewa ba zai binciki dukkan abin da gwamna mai barin gado, Ayo Fayose ya tafka a tsawo shekaru da ya yi mulkin jihar ba.
Fayemi yace idan ya hau, ba zai bi shi da takale-takalen bincike ba, amma zai bar shi da Allah ya yi masa hisabi, daidai da abin da ya aikata a jihar ta Ekiti.
Fayemi ya ci gaba da cewa zai karbi dukkan bayanan kadarori da dimbin bashin da Fayose ya bar wa jihar, ya na mai cewa ya yi amanna da cewa ita gwamnati abu ce mai bukatar a ci gaba da yi wa jama’a aiki, don haka idan ya karbi ragamar mulki a watan Oktoba, to zai ci gaba daga inda Fayose ya tsaya, sannan kuma za a ga bambanci sosai.
Kamfanin Dillancin Labari na Najeriya, NAN ya ruwaito Fayemi ya na wannan jawabi a lokacin da ya ke karbar rahoton kwamitin karbar bayanan mulki daga gwamnatin Fayose mai barin gado.
Gwamna mai jiran gado ya na bayani ne dangane da irin tulin bashin da ya ga gwamnatin Fayose ta bari.
Idan ba a manta ba, Fayose ya karbi mulki ne a hannun Fayemi, wanda a lokacin ya bar wa jihar Ekiti bashin naira biliyan 18.
Sai dai kuma a rahoton da aka kawo wa Fayemi a yanzu, an gano cewa Fayose zai tafi ya bar bashi har na naira biliyan 117.