Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya karfafa guiwar ‘yan jam’iyya yayin da ya sha alwashin cewa APC za ta lashe zaben 2019.
Lai ya ce babu wani dan takarar da ke wa jam’iyya APC wata barazana, ko ma daga kowace jam’iyya ce.
Lai ya fadi haka ne da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Benin, babban birnin jihar Edo, a yayin da ya ke shugabancin daurin auren Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsara Tattalin Arziki ta jihar, Mariam Abubakar.
“Jam’iyyar PDP ce dama ake ganin za ta iya sa APC yin gumin goshi a kokawar zaben 2019, to a yanzu kuwa PDP ta gurgunce, ko rarrafe ma da kyar ta ke iya yi.”
Daga nan sai ya ce idan aka yi la’akari da ci gaban da APC ta kawo cikin shekaru uku, to wannan ya isa a ce nasara a gare mu ta ke idan zaben 2019 ya zo.