JIJJIGAR KASA: An dakatar da fasa dutse, ginin rijiyoyin burtsatse a Abuja

0

Ministan Abuja Muhammad Bello, ya umarci da a gaggauta dakatar da ayyukan hakar ma’adinai, fasa duwatsu da kuma ginin rijijoyin burtsatse a unguwannin da jijijgar aka ta faru, kwanaki uku baya a Abuja.

Unguwannin da Ministan ya lissafa sun hada da Gundumar Garki, Maitama da kuma Mpape.

Mazauna yankunan Mpape da Maitama ne dai suka fara jin rugugin wannan jijjigar kasa a ranar Laraba da dare da kuma Alhamis da safe.

Amma ya zuwa ranar Juma’a da safe kuma, sai abin ya shafi har da yankunan Durumi da kuma Jabi a cikin Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Mutane da dama da aka yi hira da su, duk sun tabbatar da faruwar wannan jijjigar kasa a cikin Abuja.

Sannan kuma a unguwannin cikin garin musamman a cikin kasuwa ko gidajen cin abinci har ma da wuraren shakatawa da suka hada da mashaya, kusan labarin jijjikar kasar ake ta yayatawa tun bayan faruwar al’amarin wanda ya firgita mazauna birnin sosai.

Cikin wata takarda da Sakataren Yada Labarai na Ministan Abuja mai suna Sosmos Uzodinma ya sa wa hannu, Ministan ya bada umarnin a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a unguwar Mpape, inda jijjigar ta fi afkuwa sosai.

Binciken gaggawa da aka fara yi ya nuna cewa zai iya yiwuwa yawan fasa duwatsu, hakar ma’adinai da kuma ginin rijiyoyin burtsatsen da ake yi da injin mai ginar kasa, su ne su ka haifar da jijjigar kasar.

Daga nan sai ministan ya dakatar da irin wadannan hake-hake har sai bayan da aka kammala binciken gono takamaimen musabbabin wannan jijjiga wadda ta tada hankulan mazauna Abuja.

Share.

game da Author