Abu dai kamar almara kulle-kullen da ake ta shirya wa domin a dawo da korarren shugaban hukumar SSS Lawal Daura ya tabbata sai kara kulluwa ya ke yi.
A halin da ake ciki yanzu Shugaban hukumar Matthew Seiyefa da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari sun saka kafar wando daya domin kuwa Kyari ya umarci Seiyefa ya dawo da wasu daga cikin darektocin hukumar da ya tura hutun ritaya.
Sannan kuma ya umarce shi da ya tabbata sai ya sami amincewar fadar shugaban kasa kafin ya aiwatar da wasu ayyuka a hukumar.
Kyari ya umarci Seiyafa da ya dawo da darektocin da ya dakatar a wasu jihohin kasar nan maza-maza.
Seiyefa ya ce ba zai bi wadanna umarni ba domin kuwa hukumar baya hurumin Abba Kyari, da ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron Kasa Zai yi mu’amulla. Cewa ofishin SSS din na karkashin ofishin ne.
Wasu da dama daga cikin jami’an hukumar sun ce idan har aka dawo da Daura toh zasu tattara nasu-ina-su su hakura da aikin haka nan.
Bayanai sun nuna cewa ana kokarin dawo da Lawal Daura ko ta halin kaka ne domin ya jagoranci hukumar da jami’an ta a lokacin zabe da ya kunno kai.
Majiyar mu sun shaida mana cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai yi na’am da tsige Daura da mataimakin sa Yemi Osinbajo ya yi a lokacin da yake hutu a Landan ba.