Hukumar Alhazai ta kasa(NAHCON) ta bayyana cewa ta kammala jigilar alhazan Najeriya daga kasar Saudiyya.
Hukumar ta bayyana cewa a bana an fara aikin dawo da Alhazan ne daga ranar biyu ga watan Satumba da alhazan Abuja.
Hukumar ta kammala jigilar alhazan ne a lokacin da jirgin saman ‘Flynas Airline’ ya sauka da ma’aikata 100 da ya dauko daga kasar Saudi a Abuja.
Hukumar NAHCON ta bayyana cewa kafin nan jirgin ‘Medview MEV 3325’ ya dawo da alhazai 133 da ma’aikatan NAHCON 9 a Abuja da karfe4:35 na safiyar Litini.
Bayan haka shugaban hukumar Abdullahi Mohammed ya bayyana cewa sun kafa sabuwar kwamiti domin fara shirye-shiryen hajjin badi.
A karshe ya ce a bana jiragen sama sun yi sawu101 ne a jigilar alhazai 38,005.
Discussion about this post