Kamfanin sarrafa magungunan alluran rigakafi (GAVI) ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta yi tattalin tallafin da suke samu daga Kamfanin da yin amfani da shi yadda ya kamata.
Jami’ar gidauniyar Bill da Melinda Gates, Vio Mitchel ta bayyana haka a taron samun madafa game da yin allurar rigakafi a Najeriya da aka yi a Abuja a yau Litini.
Mitchel ta bayyana cewa yanke hukuncin ci gaba da tallafa wa fannin kiwon lafiyar Najeriya ba karamin nauyi ne suka kara wa kan su ba domin hakan zai sa su rage tallafin da wasu kasashen duniya ke samu daga su.
Najeriya ta fito daga yanayi na tabarbarewar arzikin kasa da ta yi fama da shi wadda
Mitchel ta ce bisa ga wannan dalili bai kamata a ce har yanzu tana samun tallafi daga GAVI ba.
Ta ce da dalilin haka take kira ga gwamnatocin kasar da su yi amfani da tallafin da suke samu daga GAVI yadda ya kamata cewa za a dakatarda bada wannan tallafi ne bayan shekaru 10 masu zuwa.
Bayan haka shugaban hukumar kula da aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya ta kasa (NPHCDA) Faisal Shuaib ya furta cewa za a yi tattalin tallafin da suke samu daga Gavi domin bunkasa yin allurar rigakafi a kasar.
A karshe jami’ar GAVI ta ce za su ci gaba da hada hannu da Najeriya don ganin sun bunkasa yin allurar rigakafi a kasar.