Tsohon shugaban masu rinjaye na makalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa duk barazana ce Saraki yake yi amma Najeriya ta fi karfin sa.
Ndume ya furta haka ne da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Abuja.
Ndume ya ce ko da wasa kada Saraki ya taba tunanin shi sa’an Buhari ne wai har zai gwada karfin siyasa da shi.
” Eh, zai iya cin zabe a jihar Kwara amma fa ba duk Najeriya ba. Da kuma kila yankin Arewa ta tsakiya in da zai ce nan yankin ya fito.
” Mutumin da bai iya rike majalisa ba ta yaya zai iya rike kasa.
” Idan aka ce an saka Buhari da Saraki a ma’auni, ay kowa ma ya san ruwa ba tsarar kwando bane. Buhari ya fi shi zama abin karbuwa.
Ndume ya kara da cewa Saraki ba mutum bane da za a amince da ganin yadda yayi ta yi wa gwamnatin Buhari zagon kasa.
” Idan ka duba a kasashe irin Amurka wanda shugaban majalisar dattawa ne mataimakin shugaban kasa. Ashe da haka muma muke yi da abin da zai rika yi wa gwamnatin da yake kai.
Idan ba manta ba Saraki da Ndume wadda makusantan juna ne sun babe ne tun bayan rashin jituwa da ta shiga a tsakanin su da har yayi sanadiyyar dakatar da Ndume da majalisar na tsawon lokaci.
Tun daga wannan lokaci babu ruwan wani da wani a tsakanin su.
Discussion about this post