Har yau hukumar ‘Yan sandan Najeriya na tsare da tsohon Darakta-Janar na Jami’an Tsaron SSS, Lawal Daura kwanaki 37 tun bayan Mukaddashin Shugaban Kasa a lokacin, Yemi Osinbajo ya tsige shi tare da tasa keyar sa aka tsare.
Wasu masu rajin kare hakkin dan adam da suka zanta da PREMIUM TIMES a kan halin da Daura ke ciki, sun bayyana cewa ba daidai ba ne a ci gaba da tsare shi har tsawon lokaci haka a hannun ’yan sanda. Sun ce yin hakan ma karya dokar Najeriya ce.
A ranar 7 Ga Agusta ne aka kama Daura, jim kadan bayan da Yemi Osinbajo ya tsige shi, dangane da wasu laifuka da suka jibinci zarge-zargen rashawa, makarkashiya, zagon-kasa, amfani da ofishi da mukamin sa ya na karya ka’idojin aiki da kuma cin amana.
Tsege Lawan Daura ya biyo bayan wani farmaki da jami’an DSS suka kai inda suka mamaye Majalisar Tarayya. Wannan farmaki kuwa ya jawo tsangwama da tofin Allah-tsine ga gwamnatin Muhammadu Buhari, wanda a lokacin ya na Landan ya na hutun kwanaki goma.
An ce Lawan Daura ya tura SSS a majalisar tarayya ba tare da neman izni daga ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara a Harkokin Tsaro ba, ofishin da shi ma ya na karkashin fadar shugaban kasa ne.
Osinbajo ya umarci a tsare Lawan Daura domin a samu damar binciken badakalar sa da ake zargin ya tafka.
Bayan tsare shi da aka yi kwana biyu a wani gida, PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa a sake shi, tare da yi masa daurin-talala a gida, wato ana sa-ido da duk irin motsin da ya yi ko wadanda ya ke mu’amala da su.
Akwai lokacin da Sufeto Janar Ibrahim Idris ya rubuta wa Osinbajo rahoton cewa ana tsare da Daura a wata ma’ajiya a cikin Garki, Abuja, sai dai ba a sani ba ko har yau a can ya ke, ko a’a.
Wani babban jami’in tsaron da ya taba samun Lawal Daura a inda ya ke tsare a wani gida mallakar jami’an tsaro, y ace a Abuja ya ke tsare, amma ana barin masu kai masa ziyara shiga, har ma da iyalan sa ba a hana su kai masa ziyasa.
Kakakin ‘Yan sanda Jimoh Moshood bai amsa tambayar da PREMIUM TIMES ta yi masa dangane da dalilin sun a tsare Lawal Daura kwanaki 37 ba tare da gurfanar da shi kotu ba.
Lauyoyi da dama irin su Mark Jacobs da Nana Nwachukwu, sun ce ba daidai ba ne a ci gaba da tsare wanda akae zargi da aikata laifi fiye da sa’o’i 48, ba tare da an kai shi kotu ba.
“Ni ina ganin cewa kawai akwai wata kullalliya da kutunguilar tsare Lawan Daura, domin an ma hana shi ya ce komai. Kuma ba mu ma sani ba ko ya na da lauya, domin har yau ba mu san wanda ke kare shi ba, idan ma har akwai.
“Ba mu san kuma irin hukuncin da za a yi masa ba, domin dai farar hula ne shi, ba soja ba, ballantana a yi masa hukunci a asirce. Ko ma dai me kenan, ana tauye masa hakkin sa da ‘yancin da doka ta ba shi.” Inji Nana.
Daura, dan shekara 65, ya zama shugaban SSS ne tun cikin 2015 da Buhari ya nada shi.
Zamanin sa ya kasance zamani ne na kame-kamen jama’a ana kullewa ba tare da hukunci ba.
Ya rika damke jama’a da sauran ma’aikatu ana tsarewa a tsawon lokaci ko da kuwa kotu ta ce a saki wanda aka tsare din.
Shi ya tsare dan jarida Jones Abiri da Sheikh Ibrahim El-zakzaky, uwargidan sa Zeenat da Sambo Dasuki, wadanda har yanzu su biyun duk su na a tsare.