Kungiyar ‘yan kasuwan Sheikh Abubakar Gumi dake Kaduna sun karyata rade-radin dake zagayawa wai wata kungiyar masu kasuwanci a Kasuwar ta tsame kanta daga cikin su, cewa wai ba su cikin wadanda suka siya wa gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai fom din takara.
Wata kungiyar masu kasuwanci a kasuwar Sheikh Gumi karkashin shugabancin Alhaji Falalu Musa Maidoya, Alhaji Gafai Boska da Mr. Thomas Yakubu sun fitar da takarda cewa ba su tare da wadanda suka siya wa gwamna El-Rufai fom din tazarce.
Kungiyar ‘yan kasuwan Sheikh Gumi sun bayyana cewa basu san wadannan mutane ba sannan wannan kungiya basu san da ita ba.
Kamar yadda yake a takardar da shugaban kungiyar Ibrahim Daudawa ya saka wa hannu ya ce su basu san wadannan mutane ba.
” Bamu san wadannan mutane ba kuma muna rokon su da su bayyana fuskokin su kowa ya gansu. Mutane ne da basu san zaman lafiya, suna neman su tada fitina ne a inda bata.
Daudawa ya ce suna so su sanar wa mutane cewa basa tare da wadannan mutane sannan basu tare da su.
” Bayan haka su sani cewa mun sanar wa jami’an tsaro domin su gudanar da bincike a kai.