Ambaliya ta ci rayukan mutane takwas a Gombe

0

Hukuma Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe, ta bayyana cewa ambaliya ta ci rayukan mutane takwas a tsakanin watan Yuli zuwa Agusta na wannan shekara.

Mataimakiyar Daraktan Hukumar a bangaren ceto, Lamis Benjamin ce ya bayyana haka a lokacin da ta ke tattaunawa da manema labarai yau Alhamis a Gombe.

Ta ce daga cikin su uku sun rasa sayukan su ne yayin da ake sheka wani ruwa kamar da bakin-kwarya a unguwannin Jekadafari, Nasarawo da Tudunwada a cikin garin Gombe, ranar 27 Ga Mayu.

Ta ce sauran biyar kuwa sun rasa rayukan su ne a yayin ambaliyar ranar 16 Ga Agusta, a Cham, Balanga da kuma wasu gidaje 60 da ambaliyar ta lalata.

Daga nan sai ta ce hukumar ta ta raba kayan agaji har buhuna 1200 na masara ga wadanda ambaliyar ta shafa a yankunan Balanga da Billiri.

An bai wan a kauyen Komta buhu 150, na kauyen Yaba an ba su buhunan masara, haka kuma an bayar a kauyukan Cham, Jessu da Yalde.

Share.

game da Author