Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta kafa kwamitoci uku da ta dora wa aikin fara shirye-shiryen tafiya aikin Hajji na shekara ta 2019 mai zuwa.
Shugaban Hukumar, Abdullahi Mohammed ne ya kafa wadannan kwamitoci ranar Juma’a a Makkah, Saudi Arabiya.
Cikin wani jawabi da kakakin hukumar mai suna Fatima Usara ta fitar, ta ce kwamitocin sun kunshi jami’an NAHCON da kuma jami’ai daga Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihohin kasar nan, “an kafa su ne domin su fara shirin aikin Hajji na 2019, da kuma shirin masaukan da mahajjata za su zauna idan Allah ya kai mu Hajjin ta badi da kuma sauran shirye-shiryen da suka wajaba a biranen Makkah da Madina..
Sanarwar ta kara da cewa Mohammed ya gana da jami’an Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihohi inda ya nuna musu jin dadin yadda sa gare su, ga daukacin Mahajjata Gwamatin Saudi Arabiya da kuma Shugaba Muhammadu Buhari dangane da gagarimar nasarar da aka samu a lokacin gudanar da aikin Hajjin bana da aka kammala kwanan nan.
Shugaban na Hukamar Alhazai ta Kasa ya jinjina wa Gwamnatin Saudiyya, domin a ta bakin sa, ya na da wuya a ce a kula da milyoyin jama’a da suka fito daga jinsina da kasashe daban-daban a inda suka taru wuri guda har a samu nasarar kulawa da lafiya da tsaron su.
Amma duk da haka inji shi, Saudiyya ta yi rawar ganin samun wannan nasara.
Daga nan kuma ya sha alwashin cewa an ba da darewa ba za a kammala jigilar Alhazan Najeriya zuwa gida.