Jam’iyyar PDP a jihar Zamfara ta tsaida tsohon dan majalisar tarayya, Bello Matawallen Maradun dan takaran ta na gwamnan jihar Zamfara.
Janar Aliyu Gusau ne ya bayyana Matawalle ga ‘ya’yan jam’iyyar inda ya ce sun samu daidaituwa ne a tsakanin ‘yan takara biyu da suka fito neman kujerar.
” Mu a jam’iyyar PDP ‘yan takara biyu ne kacal suka fito takarar gwamnan jihar. Ba kamar wasu jam’iyyun ba da ‘yan takara ke neman yi musu ambaliya.
” Bayan wannan kuma doke mu tabbata mun tsayar da ‘yan takarar da za su karbu a wajen mutanen jihar a duk kujerun da zamu fitar da ‘yan takarara.
A jawabin sa, Sahabi Yau ya ce ya hakura da takara ne ganin yadda manyan jam’iyyar suka sa baki da ya hakura wa Bello Matawalle.
” Ni dan jam’iyya ne mai biyayya, kuma saka baki da manya suka yi na daga cikin dalilan da ya sa na hakura.
Shi ko Matawalle a nashi tsokacin, jinjina wa Yau yayi bisa hakura da ya yi masa sannan ya ce idan har Allah ya basu nasara za su fi maida hankali ne wajen kau da matsalan tsaro da jihar ke fama da shi da kuma inganta harkokin mutanen jihar.