An saki wakilin PREMIUM TIMES, Samuel Ogundipe

0

A safiyar Juma’a ne aka saki wakilin PREMIUM TIMES da rundunar ‘yan sanda ke tsare da tun ranar Talata tana tuhtumar sa da ya fadi inda ya sami bayanan wani labari da PREMIUM TIMES ta wallafa a shafin ta.

A safiyar Juma’a an sake komawa wannan kotun majistare dake Kubwa, inda Lauyan Samuel ya bukaci a bada beli dan jaridar.

Alkalin kotun Abdulwahab Mohammed ya amince a ba da belin Samuel kan naira 500,000 da wani mazaunin kusa da kotun.

A ranar Talata ne rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tsare daya daka cikin wakilin jaridar PREMIUM TIMES mai suna Samuel Ogundipe a hedikwatar ta na SARS dake Abuja.

Babban dalilin da yasa ake tsare Samuel kuwa shine wai suna so ya bayyana musu asalin inda ya sami bayanai na wani labari da jaridar ta wallafa a makon da ya gabata.

Hukumar ‘Yan sanda sun nemi Samuel ya bayyana musu wanda ya bashi wadannan takardu da Sifeto Janar Idris Ibrahim ya mika wa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

A wasikar, Sufeto Ibrahim ya bayyana yadda Lawal Daura ya rika cin karen sa babu babbaka a hukumar SSS da ya shugaban ta.

Duk da cewa ba jaridar bace kawai ta rubuta wannan labari, Rundunar ‘yan sanda ta karkata zuwa ga jaridar domin wani shiri na yi mata bita da kulli.

A hedikwatar ‘yan sandan, tare da babban editan jaridar Mojeed Musikilu, ya yi kokarin bayyana wa jami’an ‘yan sandan cewa doka ta ba dan jarida kariya na kada ya bayyana inda ya samu bayanan sa, Sannan ya yi musu tuni da hakan da suke bukata daga wurin Samuel zai iya tozarta Najeriya a Idanun duniya. Da bude bakin sa dan sandan dake tare da su a wannan ofishi mai mukamin DCP, cewa yayi shi fa ‘Najeriya ba ta dame shi bane. Kawai abin da yake so a gaya masa inda aka samu wannan bayanai.

PREMIUM TIMES ta yi kira ga mukaddashin shugaban kasa da ya gaggauta bada umarni a saki wannan wakili na ta wato Samuel Ogundipe.

Bayan haka, kungiyoyin kare hakkin dan Adam na duniya sun yi tir da wannan abu kuma sun yi kira da a gaggauta sakin dan jaridar.

Jim kadan bayan sun tsare Samuel Ogundipe, sai kuma aka kulle asusun ajiyar sa na banki. Da shima haka saba dokar kasa ce.

Share.

game da Author