2019: An kaddamar da sabuwar cibiya domin magoya bayan Buhari da ‘yan Najeriya

0

A shirin tunkarar zaben 2019 da aka maida hankali yanzu, mai taimakawa shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan sabbin Kafafen yada Labarai, Bashir Ahmad, ya sanar da kaddamar da sabuwar cibiya ta yanar gizo domin magoya bayan Buhari da ‘yan Najeriya su sami daman tattaunawa a tsakanin su, sanin ayyukan da gwamnatin Buhari yayi da wadanda ake kai a yanzu.

Cibiyar mai suna Buhari New Media Centre (BNMC) za ta yi aiki ne a yanar gizo (http://www.buharicentre.com).

An tsara shafin yanar gizon ne domin ya samo wata cibiyar magoya bayan Shugaba Muhammadu Buhari, da kuma saukake hanyar yada nasarorin da gwamnatin ke samu, da kuma bada damar musayar ra’ayoyi, samun ingantattu kuma tabbatattun bayanai, akai-akai game da yadda ake gudanar da harkokin mulki.

Akwai sashin da ya tattara dukkan magoya bayan Shugaba Buhari, musamman a shafukan sababbin kafafen yada labarai a cikin shafin yanar gizon mai suna BNMC Community, za a same sashen a nan (http://www.cummunity.buharicentre.com).

Wannan sashe zai bawa yan Nijeriya musamman magoyon bayan Shugaba Buhari, da jam’iyyarsa ta (APC) damar kirkirar wani shafi cikin sauki da zasu rika mu’amala da junansu a kullum, ciki har da musayan rubutu daga wannan shafin zuwa wancan duk a kafafen sada zumunta na zamani. Membobin wannan kafar zasu kuma iya tattauna muhimman batuttuwa game da abinda ya shafi yadda ake gudanar da mulki da kuma al’amurar da suka shafi kasa baki daya. A wannan shafin yanar gizon akwai bangare na yan sa kai wato Volunteer, inda yan Nijeriya zasu iya wayar wa mutane kai domin sake zaben Shugaba Buhari a 2019.

BNMC tana da zauren sada zumunta na whatsApp, wanda zai hada dimbin magoyon baya, dake jihohin kasar nan 36 da kuma birnin tarayya Abuja, zai bawa shafin yanar gizon tabbatar da sahihai da kuma ingantattun bayanai game da manufofin wannan gwamnati don samun kyakyawar sakamako.

Cikakkun membobin BNMC dake da gogewa wurin amfani da shafukan sada zumunta na zamani zasu kasance cikin shirin BNMC na yawon rangadi, wanda zai basu damar su je su ganewa idon su irin dimbin nasarori da wannan gwamnatin ta samu a wurare daban-daban a faɗin kasar nan da kuma yadda yan Nijeriya suka amfana da ayyukan.

Shugaba Muhammadu yana cike da daunar yan Nijeriya yana kuma da burin ganin cewa ya ciyar da kasar nan gaba, ta yadda ya bada fifiko wurin kare rayuka da dukiyan al’umma, tare da samar da tattalin arzikin da talakawa marasa zasu jidadi sakamakon yaki da yakeyi da masu sace dukiyar kasa da ya kassara da dama ya daɗaɗawa ƴan kalilan.

Yi kokari ka kasance cikin wannan gida na BNMC.

Share.

game da Author