Kashi biyu bisa uku na ‘yan Najeriya na fama da rashin tsaftataccen ruwan sha – Bincike

0

Jami’in asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) Zaid Jurgi ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta samar wa mutanen kasar tsaftataccen ruwan sha da ake fama dashi a kasar.

Ya fadi haka ne a taron makon ruwa da aka fara tun a ranar 26 ga watan Agusta da aka fara a kasar Stockholm domin tsara hanyoyin samar da tsaftattaccen ruwan sha ga mutanen duniya.

Jurgi ya bayyana cewa rashin samun tsaftataccen ruwa matsala ce dake neman ya yi wa gwamnatocin duniya katutu idan ba an gaggauta daukan mataki ba.

Ya ce bincike ya nuna cewa a duniya gaba daya mutane biliyan 2.1 na fama da rashin tsaftataccen ruwan sha sannan wasu biliyan 4.5 na fama da matsalolin rashin tsaftataccen muhalli.

Ya ce a Najeriya kuwa kashi biyu bisa uku na fama da rashin tsaftataccen ruwa.

Jurgi yace rashin samun tsaftataccen ruwa na daya daga cikin matsalolin dake cutar da kiwon lafiyar mutane musamman yara ‘yan kasa da shekara biyar sannan da kawo talauci da yunwa a Najeriya.

” Bincike ya nuna cewa a Najeriya jihohi da dama kan yi fama da bullowar cututtukan da ake kamuwa da su sanadiyyar amfani da ruwa mara tsafta. A lissafe gwamnatin Najeriya za ta bukaci dala biliyan takwas don ganin hakan ya faru.

Share.

game da Author