Ma’aikatar Harkokin Gona da Raya Karkara, ta dora alhakin tsada da karancin shinkafar da ake nomawa cikin gida a kan matsalar tsarin raba shinkafar daga masu cashe ta zuwa kasuwa.
Mataimakiyar Daraktar Kula da Safarar Shinkafar ce, Fatimah Aliyu, ta bayyana haka yau Laraba a Abuja.
Ta yi wannan bayani ne a wurin taron shekara-shekara, na biyu na Gidauniyar A. Kufour Foundation (JAKF).
Ta ce kasuwar shinkafar cikin gida na samun karbuwa sosai, sai dai kuma su masu cashe shinkafar na tsoron tula shinkafar kasuwanni ne, saboda tsoron karyewar farashi idan ta yi cimbu saboda gasa tsakanin ‘yan kasuwa masu shigo da shinkafar waje.
Ta ce sun a gudun karyewar alkadarin shinkafar gida ne idan aka kwatanta da ta waje, shi ya sa masu cashe ta ke baya-baya da raba ta cikin kasuwanni har ta wadata.
Ta ce sannan kuma wasu na cewa shinkafar da ake shigowa da ita daga waje ta ma fi ta gida arha da kuma rahusa.
Su kuma masu casar shinkafa na dora alhakin tsadar ta gida a kan tsadar kayan aiki da kuma tsadar aikin casa da gyaran ta, matsalar rashin dawwamammiyar wutar lantarki, tsadar sufuri ko jigilar shinkafar zuwa kasuwanni da kuma fasa-kwaurin da ake yin a shinkafar waje.
Shi kuwa Rafi’u Lawal, kira ya yi da gwamnati ta shigo da wani tsari da zai tilasta wa ‘yan Najeriya cin shinkafar gida, kamar yadda kasar Tanzaniya ta yi.