Barawon da barci ya kwashe a wajen sata, na nan yana sharara barcin yau mako guda kenan

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta sanar cewa ta kama wani mutum dake garkuwa da mutane da ya yanke jiki ya fadi a wajen sata ya fara sharara barci.

Ana zargin barawon yayi mankas ne da kwayar Tramaol kafin su tafi sata.

Kakakin rundunar Femi Joseph ya bayyana wa PREMIUM TIMES haka ranar Asabar inda ya kara da cewa mutumin ya yi kwanaki shida yana barci a gadon asibiti.

Joseph ya ce sun kama barawon ne yana kwance a kasa a shagon siyar da magani bayan shi da abokinsa sun yi kokarin sace mai shagon a ranar 5 ga watan Agusta.

” Bayanai sun nuna cewa bayan sun shiga shagon sai wannan mutum ya yanke jiki ya fadi kasa, shi kuma abokin na sa ya tsere kafin jami’an tsaro su iso wurin.

” Bayan mun yi kokarin ya farka daga barci amma inaa, shine muka tattara shi muka garzaya da shi asibiti.

” A yanzu haka da muke magana yana nan bai tashi daga barcin ba.”

Jaridar ‘Punch Newspaper’ ta ruwaito cewa wannan mutum ya sha milligram 400 na kwayar Tramado ne shi ya sa yake ta sharba irin wannan barci.

Sai dai kuma wasu likitoci da muka zanta da su sun ce kwayar Tramadol ba ya sa mutum ya yi irin wannan barci mai tsawo haka. Sun ce kamata ya yi a gudanar da gwaji domin tabbatar da abin da ya sa wannan mutum da yake ta barci har na tsawon mako guda.

Akwai yiwuwa ya gauraya kwayoyin da yake sha da wasu kwayoyi amma bisa ga sanin mu Tramadol bata sa mutum barci irin haka.

Share.

game da Author