Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya tausa matasan mazabar sa bayan hana su kada kuri’a da aka yi a zaben Bauchi.
Yau Asabar ne ake gudanar da zaben cike gurbi na kujerar sanatan da zai wakilci shiyyar Bauchi ta Kudu a majalisar Dattawa.
Shi kan sa Dogara an hana shi kada kuri’a wai shima yayi lattin zuwa.
Sai dai kuma an rufe zabe a mazabar Yakubu Dogara ne tun karfe 2:20 na rana inda daga nan babu wanda aka yarda ya jefa kuri’a.
Abin da ya kai ga wasu daga cikin masu zabe suka tada husuma a wannan mazaba.
Da yawa daga cikin su sun koka cewa sai da suka tafi gonakin su kafin nan suka zo rumfunar zaben.
Sai dai duk da haka ba a yarda sun yi zaben ba.
Dogara ne ya kwantar musu da hankali ya nuna musu cewa ba zai yiwu su iya yin zaben ba, cewa shi ma kan sa bai samu daman yin zabe ba.