Duk da cewa dan takarar Sanata karkashin jam’iyyar APC, a zaben cike-gurbin Shiyyar Daura da ke jihar Katsina, ya shafe kusan awa uku a rumfar zabe, a haka ya koma gida bai jefa kuri’ar sa ba.
Ya sha alwashin cewa zai kare muradin APC ko da abin zai kai shi ga sadaukar da ran sa.
Babba-Kaita, ya isa mazabar Firamare ta Bakin Kasuwa da karfe 12:15, amma har lokacin dda ya bar wurin karfe 3:10, bai samu dama jefa kuri’ar sa ba.
A lokacin da ya isa wurin an buda masa layi, aka yi masa alfarma domin ya jefa kuri’a, amma sai ya ce ya gwammace ya tsaya ya bi layi.
Can bayan misalin kamar awa daya ya na tsaye, sai ya fice daga layi, sai wajen 2:49, lokacin da layi ya je kan sa, ya sake ficewa inda ya ba jami’an zabe mamaki, shi kuma ejan na PDP ya nuna rashin jin dadin sa.
Da ya ke magana da manema labarai, Kaita ya bayyana cewa akwai bukatar APC ta kara samun yawan sanatoci domin domin jam’iyyar ta kara jajjadada manufofin ta.
Duk da wannan, ya ce shi bai damu da yawan ficewar da wasu ke yi daga jam’iyyar APC ba.

Ya ce masu ficewa idan ka bi su a mazabun su ma ba su da magoya baya.
“Na shiga takara domin ina so na samu nasarar shiga Majalisar Dattawa don na kare muradin jam’iyyar ta. Kuma zan iya sadaukar da rai na domin yin haka. Zan iya sadaukar da rai na, domin na san shugaban kasa da gwamnatin APC sun yi iyakar kokarin su wajen kawo canjin da kasar nan ke bukata.
Da aka tambaye shi me zai yi idan ya ci zabe, sai ya ce ai ya ma ci zabe ya gama.
Har zuwa lokacin da aka rubuta wannan labari, Ahmed Babba Kaita bai jefa kuri’ar sa ba.
Discussion about this post