Ba mu da kudaden gudanar da ayyukan ofis – Hukumar Sauraren Korafe-korafe

0

Babban Kwamishinan Hukumar Sauraren Korafe-korafen Jama’a ta Kasa, Chile Igbawua, ya ce rashin kuddade na kawo wa Hukumar sa tsaikon gudanar da bincen korafe-korafen da aka kai wa hukumar.

Igbawua ya bayyana haka yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai, a jiya Alhamis, a Abuja.

A wurin ne ya yi musu bayanin rahotannin da ya tattara daga kwamishinonin hukumar na kowace jiha 36 na kasar nan.

Daga nan kuma ya kara da cewa hukumar na fuskantar matsanancin rashin kayan aiki, musamman motocin sufurin da za a rika zirga-zirgar gudanar da ayyukan ofis.

“Yanzu haka mu na da bukatar zagayen kananan hukumomin kasar nan, domin gani da ido halin da ofisoshin hukumar da ke kananan hukumomi, amma babu halin yin haka, saboda babu motocin da za mu yi wannan zirga-zirgar.”

Ya ci gaba da cewa, amma dai tunda an rigaya an sa wa kasafin kudin 2018 hannu, to su na da yakinin cewa za su samu wadatattun motocin zirga-zirga domin gudanar da ayyukan ofis.

“su kan su kwamishinoni na jihohi su na bukatar wadannan motoci. Amma duk da haka ina jinjina wa kwamishinonin saboda irin namijin kokarin da suke yi, duk kuwa da matsalolin da su ke fuskanta.

Ya ce daga watan Janairu, 2918 zuwa yau, samu korafe-korafe sama da 500, wadanda yawancin su duk an shawo kan su.

Share.

game da Author