Sabon Daraktan SSS ya yi alkawarin duba batun tauye ’yanci da hakki a hukumar

0

Darakta Janar Mai Riko na Hukumar SSS, Matthew Seiyefa, ya bayyana cewa hukumar ta sa za ta sake bibiyar korafe-kaorafen zargin tsare jama’a a tsarin take doka da kuma tauye wa tsararru ‘yanci da karya ‘yancin dan Adam da hukumar ke yi.

Seiyefa ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a karon farko a ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce hukumar tsaro ta SSS za ta tsaya a kan aikin da aka san ta da shi watau kwarewa wajen kare muradin kasar nan.

“Mu na korarin saisaita batutuwan mummunar fahimta da bahaguwar fassara da jama’a ke yi ga ayyukan SSS, da aka rika yi musamman kwanan nan, ciki har da tsare wasu da kuma kamen da ake wa kallon danne hakkin dan Adam ne.”

“Za mu mutunta kima da ‘yanci wata kungiya ko gungun jama’a ko kuma daidaikun mutane, matsawar su na da halastacciyar damar a yi musu hakan.

“Za mu yi aiki a bisa tsari da sharuddan sigar ayyukan da aka gindaya mana daidai da nauyin auyyukan da aka dora mana na tsaro da kuma hana kawo wa Najeriya barazana.

Dangane da tsare Sambo Dasuki, Seiyifa ya ce ba zai gaggawar cewa wani abu tunn yanzu ba, tunda a yanzu ne ma ya fara bin diddigin batun na Dasuki, da sauran batutuwan da ke gaban sa.

A karshe ya ce an fara duba yadda za a nada wa hukumar SSS kakakin yada labarai.

Dama PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa tun da Lawal Daura ya zama shugaban hukumar ba a nada mata kakakin yada labarai ba.

Share.

game da Author