Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, ya bayyana cewa ya na maraba lale da shigowar Sanata Akpabio cikin jam’iyyar APC.
Akpabio, wanda tsohon gwamnan jihar Akwa- Ibom ne, a yanzu shi ne Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa kuma dan jam’iyyar PDP ne.
Ya na fuskantar tuhumar zargin wuru-wurun kudade da suka kai biliyoyin nairori.
“Wato ni dai ina maraba da shigowar Akpabio, saboda ita fa siyasa aba ce da ake ginawa tun daga karkara, kuma can ne tushen ta. Kuma su ma wadanda suka fice daga APC ai sun fice ne saboda wani ra’ayi na su.
“Tunda ana cewa siyasa gasa ce ta nuna yawan mambobi, to kuwa mu na marhabin da shigowar shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa. An fice daga APC, yanzu kuma wasu sun shigo APC. Kun ga an ci canjarar kenan.”
Dangane ko akwai yunkurin maida Akpabio shugaban majalisar dattawa, Lai ya ce bai san wannan batun ba.
Daga nan sai ya nanata abin da ya sha fadi a baya cewa ficewar da wasu sanatoci da wakilan tarayya masu dama suka daga APC, ba wani abin damuwa ba ne.
Ya ce kiki-kakar da aka yi har Saraki ya zama shugaban majalisar dattawa ita ce ta haifar da rikici daga bangaren zartaswa na gwamnati da kuma bangaren masu tsara doka, wato majalisar tarayya ta dattawa.
Wannan inji Lai ya kawo wa Gwamnatin Muhammadu Buhari tsaikon gudanar da wasu ayyuka a kasar nan, saboda tsaikon amincewa da wasu kudirorin ya shugaban ya mika a majalisa.
Discussion about this post