An damke wani rikaken dan Boko Haram

0

Hukumar Sojojin Najeriya ta bayyana kama wani rikaken dan Boko Haram da ake zargi mai suna Maje Lawan.

An damke Lawan a garin Banki da ke jihar Barno.

Cikin wata sanarwa da kakakin su Texas Chukwu, ya ce wanda ake zargin shi ne mai lamba 96 daga cikin jerin sunayen wadanda aka buga sojoji na nema ruwa a jallo.

Burgediya Janar Chukwu ya ce an kama Lawan ne bayan da ya shiga cikin sansanin ‘yan gudun hijira.

“A halin yanzu wanda ake zargin ya na fuskantar bincike kuma da zaran an kammala, to za a damka shi ga hukumar da ta dace domin daukar matakin gurfanar da shi.”

A wata sabuwa kuma, Chukwu ya ce sojoji sun kashe wasu ‘yan Boko Haram biyu a kauyen Borno a lokacin da aka kai musu hari, wasu kuma suka arce.

Ya kuma ce an kama kekunan hawa goma daga wadannan Boko Haram a yayin da aka fatattake shi.

Sannan kuma ya kara da cewa dakarun sun fatattaki wasu mahara a sansanin su da ke dajin Gbamjimba-Akor cikin Karamar Hukumar Guma da ke jihar Benuwai.

Share.

game da Author